Latest Post

Sabon Video Yadda Jikin Mace Yake lokaccin Al Ada – Dr Husna

YADDA JIKIN MACE YAKE:

kowace yarinya tanada uterus ( makwancin yaro ) da ovaries ( gidan kwai guda biyu ) tun haihuwar ta suna nan ashirye amma basu fara aiki ba . Lokocin da yarinya takai shekaru 12 zuwa 15, gidan kwai zaifara aiki , wato kwai nafarko zai nuna . Nunan kwai a wannan lokocin zaisa jikin yarinya ta canxa zuwa mace.

KADAN DAGA CIKIN CANJIN:

– Mamanta zai girma
– Zatafara cire gashi a hammata da kuma gabanta.
– Zatafara Al’ada.

Duk wadannan chanji yana faruwa ne domin yarinya ta samu ikon haihuwa. To ko wanne wata kwai daya yakan nuna a gidan kwai. Lokocin da kwai yafara nuna makwanci zaiyi shiri domin yakarbi kwai .

Bayan kwana goma kwai yagama nuna, zai shiga hanyar kwai zaibi hanya zuwa makwanci . A wannan lokocin acikin makwanci akoi wani Abu kamar majina cike da jini tariga ta girma dan takarbi kwai . kwai zai mutu bayan kwana daya zuwa biyu .

Bayan kwana sha biyu bayan da kwai ta mutu , majina cike da jini na cikin makwanci wanda muka fada shima zai mutu , za tafita waje tare da jini itace jinin al’adar mace.

Wannan yana faruwa ne ko wanne wata. Ko wanne wata kwai daya zai nuna a gidan kwai idan mace bata hadu da na miji ba lokocin da kwan tana da rai bato kwan zai mutu kuma zai zama jinin al’ada yafita.

Kamar yadda mukasani Jinin Al’ada tana zuwa da Dan murdan ciki ta dalilin mahaifa ke motsawa waje guda domin fitar da jinin. Da sauran alamomi Wanda ba lalle sai mun anbanta ba.

Kamar yadda mukasani wassu kan fiskanci matasaloli daban daban yayin zuwan alada ta xubar jinni diyawa  ko ciwon ciki mai tsanani (Dysmenorrhea) to wadannan matsalolin mafi yawa tana faruwa ne ta dalilin:

  1. – Shigar kwayoyin cuta
  2. – Ciwon sugar
  3. – Wassu magunguna da baikamata asha ba.
Idan ana samun wannan matsalar yakamata aje asibity.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button