Labaran Kannywood

Sabon Video Abinda yasa na maka Hadiza Gabon Kotu – Matashi

Tirkashi da dumi dumi yanzu yanzu muka Sami wata sabuwar rahoto Mai ban mamaki da ban Al ajabi yadda wani Matashi Dan kasa da shekaru 30 ya Maka Hadiza Gabon Kotu

Assalamualaikum warahamatullahi taala wabarakatuh jamaa masu albarka barkanmu da sake saduwa daku a dai dai wannan lokaccin dauke da sabon video

Wani ma’aikacin gwamnati ya maka Jaruma Hadiza Gabon a Kotu sabida taƙi aurensa bayan ta lakume masa kuɗi

Wani ma’aikaci ya kai karar jaruma Hadiza Gabon gaban Kotun Shari’ar Musulunci kan ta karya masa alƙawarin aure Bala Musa ya shaida wa Kotun sun jima suna soyayya da Gabon kuma ta masa alƙawarin aure,

shiyasa da ta nemi Kuɗi yake tura mata Lauyan da ke kare Gabon ya roki Kotu ta bashi isasshen lokaci domin ya zo da wacce yake karewa

“Daga lokacin da muka fara soyayya zuwa yanzun na kashe mata kuɗi N396,000. Duk lokacin da ta nemi kuɗi ina bata ba tare da damuwa ba ina fatan wataran zamu yi aure.” “Ta gaza zuwa Gusau, babban birnin jihar Zamfara inda nake zaune bayan na kammala duk wasu shirye-shiryen tarbarta.”

Lauyan Hadiza, Mubarak Kabir, ya shaida wa Kotun cewa wacce yake kare wa ta gaza tabbatar da gaskiyar sammacin Kotu da aka kai mata.

Lauyan ya faɗa wa Kotu cewa: “Wacce nake karewa ba fitacciyar mace ce da ke mu’amala da mutane daban-daban da niyya daban-daban. Ta na matuƙar kula da lafiyarta da tsaron kanta

Bayan haka Ƙabir ya roki Kotun ta ba shi lokaci isasshe domin ya gabatar da wacce yake karewa a gaban Kotu. Alƙalin Kotun mai shari’a Malam Rilwanu Kyaudai, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 13 ga watan Yuni, 2022.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button