Labarai

Cikakken Sabon Video Yadda Yan Bindiga Suka Kai Harin Church

‘An kulle mu a Cocin sama da mintoci 20’ – Firist yayi magana akan harin Ondo

Rev Father Andrew Abayomi, daya daga cikin limaman cocin St Francis Catholic Church, dake titin Owa-luwa, Owo, jihar Ondo, ya bayyana yadda aka kaiwa cocin hari.

Aminiya ta ruwaito adadin masu ibada da suka mutu a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai harin bam a cocin a safiyar Lahadi.

A wata hira da BBC Yoruba, malamin ya ce wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai hari a yayin da ake shirin kawo karshen hidimar ranar.

“Mun kusa kashe sabis. Har ma na nemi mutane su fara tafiya, a haka ne muka fara jin karar harbe-harbe ta bangarori daban-daban.”

“Mun boye a cikin cocin amma wasu mutane sun fita lokacin da harin ya faru. Mun kulle kanmu a cikin coci na minti 20. Da muka ji cewa sun fita ne muka bude coci muka garzaya da wadanda abin ya shafa asibiti.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button